Cryptocurrency: Makarantar da ta fara karɓar kuɗin intanet a matsayin kuɗin makaranta a Kano

cryptocurrency

Asalin hoton, Getty Images

Wata makaranta mai zaman kanta a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta fara karɓar kuɗin intanet na cryptocurrency a matsayin kuɗin makarantar da ɗalibai za su dinga biya.

Shugaban makarantar, Sabi’u Musa, ya shaida wa BBC Hausa cewa ya ɗauki wannan mataki ne don ganin yadda kuɗin intanet yake ta samun ƙarin karɓuwa a duniya.

A ranar Alhamis ne Malam Sabi’u ya fara shaida wa manema labarai wannan mataki nasa da wadda makarantar New Oxford Science Academy da ke unguwar Chiranchi ta ɗauka.

Ya ƙara da cewa hukumar makarantar ba ta ɗauki matakin ba sai da ta tuntuɓi iyayen yara don jin ta bakinsu.


Source link

Leave a Reply

%d bloggers like this: